Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan al-Shabab Sun Kai Hari Kan Wani Otel a Mogadishu


Otel din da mayakan al-Shabab suka kai hari a Mogadishu

Harin da mayakan al-Shabab suka kai kan wano otel a Mogadishu ya hallaka akalla mutane 12 da suka hada da wani kwamandan sojojin Somaliya da wakilan majalisar dokoki.

Kungiyar mayakan sa kai ta al-Shabab dake Somaliya ta dauki alhakin wani mummunan hari da aka kai kan wani O'tel a Mugadishu jiya Lahadi, inda ta halaka akalla mutane 12, ciki harda mai O'tel din, wani kwamandan sojoji da wakilan majalisar dokokin kasar guda biyu.

Hukumomi suka ce mayakan sa kan sun tada nakiyoyi da aka boye cikin wata mota a kofar shiga O'tel da ake kira Sahafi dake Mogadishu baban birnin kasar. Bayan fashewar sai yan binidga suka auka cikin O'tel din mai farin jini ga jami'an gwamnatin kasar da wasu manyan yan kasuwa.

Ministan tsaron kasar Abdulrazak OMar Mohammed ya gayawa Muryar Amurka cewa maharan wadanda dukkansu jami'an tsaro sun kashe su, suna saye da kayan sojojin kasar Burundi, wanda yace , tana yiwuwa sun samo su ne lokacinda suka kai wani mummunan hari kan sansanin sojojin na Burundin dake Leego cikin watan Yuni.

Cikin wadanda aka kashe a harin harda Janar Abdikarim Yusuf Dhagabadan, wani tsohon kwamandan sojoji wanda ya jagoranci farmakin da ya tilastawa al-Shabab barin birnin Mugadishu a shekara ta 2011. Janar Dhagabadan ya sha tsallake rijiya da baya a wasu yunkurin halakashi da kungiyar ta al-Shabab tayi.

Kakakin kungiyar Sheikh Abdilaziz Abu-Musab ya tabbatar da cewa kungiyar ce ta kai harin, a cikin wata sanarwa da ta gabatar jiya lahadi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG