Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan al-Shabab sun hallaka sojojin Somalia 32


Mayakan al-Shabab
Mayakan al-Shabab

Mayakan al-Shabab sun kai hari kan wani gari a tsakiyar yankin Shabelle dake kasar Somali jiya Lahadi da safe sun kuma sake cafke garin.

Wannan harin baya bayan nan ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Somali 22 kamar yadda wani jami'i ya shaidawa Muryar Amurka amma tare da neman a kare sunansa.

Amma su mayakan sun ce sun kashe sojoji fiye da 32 da suka hada da wani babban jami'in soji a garin Runirgood kwana daya bayan garin ya fada hannun dakarun gwamnati.

Kwamandan rundunar soji ta goma sha biyu ta kasar Somalia Mohamed Mohamud Sanay ya gayawa Muryar Amurka an yiwa sojojinsa kwantan bauna ne inda aka kashe takwas daga cikinsu yayinda sojojinsa suka kashe mayakan al-Shabab goma sha biyu. Kwamandan yace an jima wani babban jami;in sojinsa rauni kuma ya bace.

Wani jami'in Somalia da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Muryar Amurka cewa sojoji 22 aka kashe kana 10 kuma suka bace wadanda ana kyautata zaton mayakan sun kamasu kuma sun kashesu.

Ganau sun ce mayakan sun yi anfani da wata motar kunar bakin wake dake dauke da bam suka yi anfani da ita wurin kwace akalla motocin soji uku.

XS
SM
MD
LG