Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Taron Kolin Nahiyoyin Afirka Da Turai a Abidjan


Otel din Sofitel da taron koli na nahiyoyin Afirka da Turai ke gudana a Abidjan, babban birnin Cote d' Ivoire

Shugabannin kasashen nahiyar Afirka da takwarorinsu na turai, suna gudanar da wani taron koli a Abidjan, babban birnin Cote d' Ivoire domin tattauna matsalolin da suka shafi nahiyoyin biyu musamman kan batun kwararar bakin haure zuwa turai.

Shugabannin kasashen Turai da na Afrika sun hallara yau Laraba a kasar Ivory Coast don taron kolin da zai maida hankali kan batutuwan da suka shafi nahiyoyin biyu.

Daga cikin batutuwan har da hadin gwiwar tattalin arziki, da samar da ayyukan yi, da kaurar jama’a da kuma tsaro da wanzuwar zaman lafiya.

Taron kolin na kwanaki biyu da kasashen tarayyar Turai da kuma kungiyar kasashen Afrika suka fara a birnin Abidjan ya tattaro shugabannin Afirka 55.

Daga bangaren turai kuma taron ya hado mambobin kungiyar kasashen turai 28.

A lokacin wata ganawar ministocin gabanin taron da aka fara, mataimakin shugaban majalisar zartaswar Kungiyar Tarayyar Afirka, Afirka Kwesi Quatery, ya ce “muna kokari ne mu karfafa salon siyasa mai dorewa domin amfaninmu, da kuma na ‘ya’ya da jikokinmu.”

A ‘yan shekarun nan, gwamnatoci daga nahiyoyin biyu sun fuskanci kalubalen ‘yan gudun hijira da ke ratsawa ta kasashen arewacin Afirka suna tsallaka tekun Bahar Rum a kan hanyarsu ta zuwa Turai.

Hakan ya haifar da muhawara akan sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar da kuma yadda za a kare su a kan wadannan hanyoyi masu hatsari da suke bi da ke janyo mutuwar dubbansu a kowace shekara.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG