Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Al-Shabab Sun Raunata Mutane Bakwai A Mogadishu


Mutane bakwai sun ji raunuka bayan da mayakan kungiyar al-Shabab su ka kai harin roka wanda ya dira kan wani wuri a Mogadishu a jiya Lahadi, a cewar wasu 'yan Somaliya da abin ya faru a gabansu da kuma wasu jami’ai.

Rokokin da aka cillo sun fada kan bangaren Halane na filin jirgin saman mai matukar matakan tsaro wanda ke dauke da gine-ginen kungiyar hadin kan Afrika ta AU da Majalisar Dinkin Duniya a Somaliya.

Shaidu sun fada wa Sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa rokoki shida aka cillo a wuraren jim kadan bayan karfe daya na rana agogon yankin.
Kungiyar mayakan al-Shabab ta dauki alhakin kai wannan harin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG