Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Boko Haram 163 Ne Suka Fada Hannun Sojoji Makon Nan


Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Buratai a tsakiyar sojoji biyu

Rundunar sojojin Najeriya dake birnin Maiduguri dake fafatawa da 'ya'yan kungiyar Boko Haram tace ta samu nasarar cafke wasu mayakan Boko Haram su 163 kana wasu guda biyu suka mika kansu da kansu

Kwamandan rundunar mai kula da yankin arewa maso gabashin Najeriya Manjo Janar Lucky Irabor ya shaidawa manema labarai na mako mako.

Manjo Janar Irabor yace suna cigaba da samun nasarori da dama da suka hada da gano makamai daga hannun 'yan kungiyar tare da kame wasu daga cikinsu.

Sojojin sun kara yin arangama a kauyen Gulde da 'yan ta'adan a karamar hukumar Askira Uba inda suka kashe 'yan ta'adan su goma sha daya kana suka kama wasu tara da ransu, yayinda soja guda ya samu rauni.

Kawo yanzu sojojin sun samu gawarwakin 'yanuwansu goma sha biyar da suka bace can baya.

A yankin tafkin Chadi sojoji sun kashe 'yan ta'ada shida tare da cafke makamai masu dimbin yawa.

A wani taho mu gama da suka yi da 'yan ta'adan sojojin sun yi hasarar jami'ansu guda biyar kana sojoji uku suka samu raunuka.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:59 0:00

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG