Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Sake Kubutar Da Wata ‘Yar Makarantar Chibok


Hedikwatar sojojin Najeriya tace dakarun kasar sun ‘kara kubutar da wata ‘dalibar makarantar sakandare ta garin Chibok daga hannun mayakan Boko Haram.

Kakakin hedikwatar sojojin Najeriya kanal Sani Usman Kuka Sheka, shine ya tabbar da cewa sun sami kubutar da Rakiya Abubakar ‘daya daga cikin ‘yan matan da kungiyar Boko Haram ta sace sama da shekaru biyu da suka gabata.

Yace sojojin Najeriya ne suka samo ta lokacin da suka kama wasu mayakan Boko Haram, an gano ta ne cikin binciken da aka gudanar gano ta kuma aka tabbatar da cewa tana ‘daya daga cikin ‘daliban da aka sace daga makarantar Chibok.

An sami Rakiya Abubakar, ‘dauke da yaro ‘dan wata shida da haihuwa. Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan lafiyar ta kafin a mika ta ga gwamnatin jihar Borno.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG