Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Boko Haram Sun Sake Far wa Garin Kanamma A Jihar Yobe


Mayakan Boko Haram Sun Sake Kai Wani Hari
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:17 0:00

Mayakan Boko Haram Sun Sake Kai Wani Hari

Kasa da mako daya da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka afkawa garin Geidam lamarin da rutsa da dubban mutane tare da sa mutane sama da dubu 6 gudun hijra, wasu ‘yan bindiga sun sake afkawa garin Kanamma, da ke shelkwatar karamar hukumar Yunusari da maraicen ranar Alhamis.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai inda ya ce, lamarin ya auku ne a wajen garin na Kanamma.

ASP Abdulkarim, ya bayyana takaici kan yadda ba sa samun magana da jami’ansu a garin na Kanamma sakamakon rashin sabis na wayar salula, ya na mai cewa, da zarar sun same su, rundunar za ta bada karin bayani.

Wani ganau a yankin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, baya ga jin karar bindiga kusa da sansanin soji, mazaunan yankin suka fara tserewa zuwa cikin daji domin tsira da ran su.

Garin Kanamma dai na makwabtaka da Jmhuriyyar Nijar kimanin kilomita 34 daga garin Geidam inda aka fara fuskantar ayyukan 'yan Boko Haram a shekarar 2004 kafin suka koma birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno tare da fara kai mummunan hari da suka salwantar da dubban rayuka.

Karin bayani akan: jihar Yobe, jihar Borno, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.

A jihar Borno ma, mazauna garurruwa daban-daban sun sake ganin munanan hare-hare a bayan-bayan nan daga mayakan Boko Haram da ma ‘yan bindiga.

Baya ga jihohin arewa maso gabas, a arewa maso yamma kamar Kaduna, Katsina, Neja da dai sauransu na fuskantar hare-haren 'yan bindiga dadi da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Sai kuma yankin kudancin Najeriya inda haramtacciyar kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra ke kai farmaki kan jami'an tsaro da Fulani makiyaya.

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta sha alwashin murkushe miyagun da ke addabar kasar a lokuta da dama amma har yanzu hakar ba ta cimma ruwa ba.

XS
SM
MD
LG