Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Hezbollah Sun Ce Isra'ila Ta Kashe Dan Uwansu


Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Kungiyar mayakan sa kan Hezbollah na kasar Lebanon sun ce harin saman da Isra’ila ta kai ta sama ya hallaka daya daga membobinta wanda ya share shekaru fiye da 30 a gidan yarin Isra’ilan bisa zargin aikata kisan kai.

Samir Kantar na daya daga cikin daruruwan Hesbollah din da suka tafi Syria don taya mayakan Bashar al-Assad yaki bayan barkewar yakin basasa a shekarar 2011. Harin dai nay au Lahadi ya fada ne kan wani gini a Jaramana dake wata unguwar wajen gari a kudancin Damascus.

Ba dai wata tankiya da Isra’ilan ta yi akan lamarin, wacce ta sha kai hare-hare a Syria daga ‘yan shekarun baya, mafi yawanci akan tawagar da Isra’ilan kan ce suna dauke da makamai ne a hanyarsu ta shiga Syria dasu ta Lebanon.

An dai daure Kantar ne a shekarar 1979 bisa zargin kashe dan sandan Isra’ila da kuma wani mutum da ‘yarsa a yayin da matarsa kuma ta shake wani yaro ya mutu lokacin da suka buya a gidansu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG