Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Al-Shabab Sun Kai Hari Kan Wasu Sansanonin Sojojin Somaliya Guda Biyu


Mayakan Kungiyar Al-Shabab
Mayakan Kungiyar Al-Shabab

Wasu majiyoyi na mazauna yanki da kuma Jami’an Soji sun tabbatar da cewa mayakan kungiyar Al-Shabab sun kai hari suka kwace wasu sansanonin sojojin Somaliya guda biyu dake wajen Mogadishu, babban birnin kasar, da sanyin safiyar yau Lahadi.

Mazauna Kauyukan Tihsile da kuma Warmahan dake yamma da birnin Mogadishu sun ce 'Yan tsagerun sun kai hari a wadannan sansanonin guda biyu a lokaci guda.

Wata majiya daga jami’an sojojin ta bayyana kimanin jami’an sojojin gwamnati 40 zuwa 50 ne aka ajiye a kowanne sansani.

An kashe sojoji akalla guda biyu a Tihsile yayinda har yanzu ba ‘a san adadin wadanda abin yasha fa ba a Warmahan.

Wasu majiyoyin soja sun fadawa sashen Somaliya na VOA cewa karin sojojin da aka tura domin kai dauki ma wadannan sansanonin sun taka wata nakiyar da aka binne kan hanya a kusa da garin Wanlaweyn, mai tazarar kilomita 90 a yamma da Mogadishu.

Nakiyar ta kashe mataimakin kwamandan shiyya ta 6 ta sojojin Somaliya da wani babban hafsan soja guda daya, a cewar wasu majiyoyin soja. Sojiji takwas ne suka ji rauni a fashewar bam din.

Fashewar Bam din ta faru ne ga jerin motocin kafin fitowar rana, yayin da Sojojin ke tunkarar Tihsile da kuma Warmahan domin taimakawa sojojin gwamnatin da aka kaiwa hari .

Mazauna kauyukan sun tabbatar da mafi yawan sojojin gwamnati na sansanonin guda biyu sun kubuta daga harin ba tare da wani rauni ba . An sami rahoton yan tsagerun sun janye daga kauyukan.

Kungiyar Mayakan na Al-Shabab sun yi ikirarin kwace albarusai da kuma motocin sojoji guda biyu.

XS
SM
MD
LG