Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Kungiyar Daesh Sun Kwace Wani Bangare Na Yankin Duwatsun Tora Bora.


Soja Na Kewaya White Mountains Kusa Da Tora Bora, Afghanistan, Dec. 18, 2001.
Soja Na Kewaya White Mountains Kusa Da Tora Bora, Afghanistan, Dec. 18, 2001.

Ana tafka kazamin fada a yankin Tora Bora tsakanin ISIS da Taliban Da kuma sojojin sakai masu goyon bayan gwamnati.

Mayakan kungiyar Daesh ko ISIS sun kwace wani bangare na yankin duwatsun Tora Bora na kasar Afghanistan cikin daren talata a bayan kazamin fadan da suka gwabza da mayakan Taliban da wasu sojojin sa kai masu goyon bayan gwamnati.

Wannan yanki mai duwatsu yana dauke da koguna masu yawa a bakin iyaka da Pakistan. Yankin na Tora Bora yayi kaurin suna a lokacin da mayakan da Amurka suke yi ma jagoranci suka rutsa shugaban kungiyar al-Qa’ida, Osama bin laden, cikinsu, watanni kadan a bayan harin da aka kai kan Amurka na ranar 11 Satumbar 2001. Bin Laden ya tsere ya sulale cikin Pakistan.

An fara gwabza mummunan fada a yankin mako guda da ya shige a lokacin da mayakan ISIS suka far ma sojojin Taliban a wurin. Da farko, ‘yan Taliban sun fatattake su. Sojojin sa kai masu goyon bayan gwamnati suke kuma adawa da Taliban, sun shiga fadan su ma suka yaki ISIS.

Daga bisani, ‘yan ISIS sun komo suka kwace Tora Bora, sannan suka kaddamar da wani sabon farmaki kan gundumar Pachiragam, daya daga cikin gundumomi 22 na lardin Nangarhar.

Wani wakilin VOA a yankin, Zabihullah Ghazi, yace ana gwabza kazamin fada, kuma da alamu gundumar tana dab da fadawa hannun ‘yan ISIS.

Amma kuma kakakin ma’aikatar tsaron Afghanistan, Janar Dawlat Waziri, bai tabbatar da kwace Tora Bora da ‘yan ISIS suka yi ba. Yace, “mun ga karuwar ayyukan ‘yan ISIS a Chaprahar da Pachiragam tun daga jiya, amma sojojinmu suna sane da hakan.” Yace yana da kwarin guiwa sojojin Afghanistan zasu murkushe ISIS a wurin, kamar yadda suka yi a baya a gundumar Achin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG