Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Sa Kai Na Kungiyar Mai Mai Yakutumba Sun Kai Hari A Congo


Sojojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Sojojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Sojojin kwantar da tarzoma na Majalisar Dinkin Duniya na kokarin kare fararen hula a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

An tura sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a wani yankin gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, bayan wata arangama tsakanin Yan tawaye da sojojin Congo.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar yace ya tura dakarun ne wadanda ake kuma kira da MONUSCO a takaice, zuwa Ivira domin kare fararen hula da kuma hana afkuwar hari a Birnin dake kusa da Iyakar kasar da Burundi, a karshen Tafkin Tanganyika ta Arewaci.

Wakilin Sashen Faransa na Muryar Amurka Ernest Muhero yace 'yan tawayen wata kungiya da ake kira Mai Mai Yakutumba ne suka turo jiragen ruwa 4 cike da mayakan sakai ta tafkin don kai hari kan wata Gada a safiyar jiya Alhamis.

Shugaban gundumar Uvira , Sephanie Milenge Matundanya, yace dakarun kasar sun kori mayakan sa kan daga Birnin da kuma mafiya yawan kauyukan da suka kama.

Wani mazaunin yankin ya fadawa Muryar Amurka cewa Jirage masu saukar Ungulu na Majalisar Dinkin Duniya suna shawagi a yankin, kuma al’amura sun fara lafawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG