Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maza Sun Fi Mutuwa Ta Dalilin HIV A Najeriya


Wani mutum mai dauke da cutar HIV.
Wani mutum mai dauke da cutar HIV.

Bincike ya bayyana cewa maza sun fi mutuwa ta dalilin kamuwa da cutar kanjamau a Najeriya.

Bincike ya bayyana cewa maza sun fi mutuwa ta dalilin kamuwa da cutar kanjamau a Najeriya.

Darektan hukumar yaki da cutar kanjamau na kasa Farfesa John Idoko ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Abuja lokacin ziyarar babban darektan asusun tallafin na duniya.

Forfesa Idoko yace binciken da aka gudanar a babban asibitin Wuse ya nuna cewa mata ne suka fi zuwa domin gwada lafiyarsu da kuma kokarin sanin ko suna dauke da kwayar cutar HIV ko babu, yayinda maza suke gujewa irin wadannan gwaje gwajen domin basu son su san anihin lafiyarsu. Sabili da haka inji shi, maza dake dauke da cutar kanjamau basu samun magani da zai ceci rayukansu.

Darektan yaki da cutar kanjamau a Najeriya yace shan magani yana da muhimmanci ga duk wanda yake dauke da kwayar cutar HIV. Bisa ga cewarsa maza da yawa suna mutuwa saboda basu neman magani.

Frofesa Idoko yace yawan matan dake gwaji da shan magani ya ruba na mazan. Ya bayyana cewa, har yanzu Najeriya ce tafi kowacce kasa yawan jarirai da ake haifa dauke da kwayar cutar HIV a duniya, inda ake haifar kimanin jarirai dubu saba’in dauke da kwayar cutar kowacce shekara.

Ya kuma bayyana cewa hukumar yaki da cutar kanjamau ta kasa ta gabatar da wani tsari da zata gudanar cikin shekaru biyu da zai taimaka wajen samar da magunguna ga sama da mata masu ciki dubu tamanin.
XS
SM
MD
LG