Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Karamar Hukumar Shiroro Na Kauracewa Gidajensu Sakamakon Ficewar Sojoji Da Hare-haren ‘Yan Boko Haram


Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya
Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya

Daruruwan mazauna yankin Alawa ta karamar hukumar Shiroro a jihar Nejan Najeriya na ci gaba da tserewa daga gidajensu a sakamakon yadda mayakan kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kai musu hare-hare.

NIGER, NIGERIA- Rahotanni daga yankin na Alawa na nuna cewa hatta sojojin da aka jibge a karamin sansanin sojojin na Alawa a cikin daren Laraba da ta gabata sun kwashe kayansu sun bar wurin.

Wani Mazaunin yankin da ya tsallake rijiya da baya ya kuma bukaci a sakaya sunanshi ya ce kasa da mako guda mayakan na kungiyar Boko Haram suka kona garuruwa sama da biyar a yankin na Alawa san nan suka ci gaba da binne bama bamai akan hanya.

Rahotanni dai sun nuna cewa ko baya ga kashe sojoji shida a makon da ya gabata da ranar Litinin ma wasu sojojin biyu sun mutu sannan kaftin guda na sojojin yayi mummunan rauni a sakamakon wani bom da motarsu ta taka.

Hon. Akilu Kuta shugaban karamar humumar Shiroron ya ce suna cikin tashin hankali a sakamakon yadda ayyukan mayakan kungiyar ta Boko Haram ke kara yawa a ‘yan kwanakin nan.

A zantawa da Muryar Amurka shugaban na karamar hukumar shiroro Akilu Kuta ya ce tashin sojojin daga wannan yanki ya kara jefa mutanensu cikin wannan tashin hankali.

Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar sojin Najeriya akan cire sansanin sojojin na Alawa domin kuwa kokarin samun hedikwatar sojojin ta Najeriya yaci tura.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

Mazauna Karamar Hukumar Shiroro Na Kauracewa Gidajensu Sakamakon Ficewar Sojoji Da Hare-haren ‘Yan Boko Haram.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG