Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PSG Na Gab Da Lashe Kofin Gasar Ligue 1


'Yan wasan PSG na taya Mbappe murnar zura kwallo a karawarsu da Angers
'Yan wasan PSG na taya Mbappe murnar zura kwallo a karawarsu da Angers

PSG na da maki 15 a saman teburin gasar, za kuma ta lashe kofin ne a karo na 10 idan ba ta sha kaye a hannun Lens ba.

Paris Saint-Germaine (PSG) ta na kara kusantar lashe kofin gasar Ligue ta kasar Faransa yayin da za ta kara da Lens a ranar Asabar.

Lens na matsayi na bakwai ne a gasar ta Ligue 1, it ace kuma za ta kai wa PSG ziyarar.

PSG na da maki 15 a saman teburin gasar, za kuma su lashe kofin ne a karo na 10 idan ba su sha kaye a hannun Lens ba.

Kungiyar na da zaratan ‘yan wasa da suka hada da Lionel Messi, Kylian Mbappe da kuma Neymar, wadanda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito ya gansu suna atisaye a ranar Juma’ar nan.

Ita kuwa Marseille da ke da sauran wasanni biyar a gasar, za ta kamala wannan kakar wasa a matsayi na biyu.

Marseille, wacce ta taba lashe kofin gasar sau tara ta ba Rennes da Strasbourg tazarar maki shida gabanin wasan da za ta kara da Reims a ranar Lahadi.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG