Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD: Amurka da Rasha Sun Cimma Matsaya kan Makaman Guba


Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry

Kudurin hukumar tsaron Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da Rasha suka cimma matsaya idan an tabbatar dashi zai bada izinin a dorawa duk wanda ya yi anfani da makaman guba laifi a hukumance tare da yi masa tuhuma.

Amurka da Rasha sun cimma matsaya kan kudurin Hukumar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya na gano wadanda suke anfani da makaman guba a kasar Syria inji sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.

Sakatare Kerry ya bada sanarwar ce yau Alhamis a Kuala Lumpur dake kasar Malaysia jim kadan bayan ganawarsa da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a taron kolin kasashen Asiya.

Yarjejeniyar da suka cimma zata bada damar daukan matakan ladaftarwa wanda kawo yanzu babu hanyar yin hakan.

Ana kyautata zaton za'a jefa kuri'a akan kudurin mako mai zuwa lamarin da ka kai ga kafa wani kwamitin da zai binciki wadanda suka yi ruwa da tsaki wurin yin anfani da makaman guba a yakin Syria.

Kungiyar da ta hana yin anfani da makaman guba wato Organization for the Prohibition of Chemical Weapons ko OPCW a takaice na kokarin aika tawagar bincike akan hare-haren amma kungiyar da Majalisar Dinkin Duniya basu da ikon dorawa kowa alhakin yin anfani da makaman guba sai an tsayar sabon kuduri kan lamarin.

A shekarar 2013 kungiyar OPCW ta taimaka da kwashewa da lalata makaman guba da Syria ta bayyana tana dasu biyo bayan daidaito tsakanin Amurka da shugaban Syria Bashar al-Assad a kan makaman.

Amma duk da hakan ana cigaba da yin anfani da makaman guba lamarin da ya kawo damuwa. Ana zaton gwamnatin Syria nada makaman guba kamar su iska mai guba da makamantansu da basa cikin yarjejeniyar da aka cimma da can.

Shugaban Syria Bashar al-Assad na cigaba da musanta yin anfani da makaman. Maimakon hakan ma yana dora alhakin ne akan 'yan tawayen dake fafutikar kawar da gwamnatinsa.

Kasar Rasha babbar kawar Shugaba Bashar al-Assad kodayaushe tana ki kememe a dorawa gwamnatin Syria alhakin yin anfani da makaman guba da zara maganar ta kai Hukumar Tsaro wurin da za'a yi muhawa domin gano mai laifi.

XS
SM
MD
LG