Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD: Iran Ta Fara Rage Ayyukan Nukiyar Kasar


Shirin nukiliyar Iran
Shirin nukiliyar Iran

Biyo bayan yarjejeniyar da Iran ta kulla da wasu manyan kasashen duniya, yanzu ta fara rage ayyukan nukiliyar kasar

A wani rahoton da hukumar hana yaduwar makaman kare dangi ko Atomic ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayar ta ce Iran ta fara rage ayyukan Nukiliyar kasar wadanda zata iya amfani dasu wajen kera makaman Nukiliya, kamar yadda yarjerjeniyar da kasar ta kulla da manyan kasashen duniya.

Duk da haka jami'an difilomasiyya wadanda suka san abunda rahoton ya kunsa, sun yi gargadin cewa, Iran ta adana dubban na'urorin tace sinadaran Uranium wadanda zata iya sake girke su wajen ayyukan sarrafa makaman Nukiliyar.

Wasu sassan rahoton da hukumar ta mikawa Majalisar Dinkin Duniya da aka rarraba jiya Laraba, ya nuna cewa a babbar tashar Nukiliyar Iran akwai na'urori- wadanda ake kira "centrifuge" da turanci dubu goma sha daya da dari uku da takwas, amma zuwa wannan mako, an janye fiyeda dubu uku,kasa da na'urori da suke aiki lokacinda wannan yarjejeniyar ta fara aiki ranar 18 ga watan Jiya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG