Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Kwashe 'Yan Gudun Hijira 149 Daga Libya

Wasu 'yan gudun hijira da aka kwaso daga kasar Libya zuwa Malta
Wasu 'yan gudun hijira da aka kwaso daga kasar Libya zuwa Malta

Su dai ‘yan gudun hijrar, sun kwashe watanni cikin wani yanayi na tashin hankali, a wani wuri da aka ajiye su a birnin na Tripoli.

Hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ta ce ta kwashe masu gudun hijira da masu neman mafaka 149 daga Tripoli, babban kasar Libya mai fama da tashin hankali, inda ta kai su kasar Italiya domin kare rayukansu.

An kai ‘yan gudun hijira wani matsuguni ne da ke wajen babban birnin Roma a karshen makon nan.

Sun kuma fito ne daga kasashen Eritrea, Somalia, Sudan da kuma Habasha.

Daga cikinsu akwai kananan yara 65, sannan 13 daga cikinsu ba su kai shekara daya ba, a cewar hukumar ta UNHCR mai kula da ‘yan gudun hijira.

Su dai ‘yan gudun hijrar, sun kwashe watanni cikin wani yanayi na tashin hankali, a wani wuri da aka ajiye su a birnin na Tripoli.

Hakan ya sa hukumar ta hada kai da hukumomin Libya da kasar Italiya aka kwashe su zuwa mafakar da ke Italiyan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG