Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Nada Wakili Kan Rikicin Siyasar Sudan


A makon daya gabata ne dai sojojin kasar Sudan suka hambarar da dadaddan shugaban kasar Omar al-Bashir, sakamakon zanga zanga da ta yi kamari. yanzu haka Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci sojojin da su mika mulki ga farar hula cikin kwanaki 15.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ya nada mai ba da shawara na musamman Nicholas Haysom, a matsayin mai taimakawa kungiyar tarayyar Afirka ta AU, a shirin shiga tsakani da take yi a rikicin siyasar Sudan, inda dakarun kasar suka kifar da gwamnatin dadadden shugaban kasar Omar Al Bashir a makon da ya gabata.

Antonio Guterres, ya fadawa shugaban majalisar zartarwar kungiyar ta AU, Moussa Faki Mahamat cewa, mai ba da shawara Haysom zai zamanto cikin shiri a duk lokacin da ake bukatarsa.

Shi dai Haysom ya kasance shi ne babban jami’in majalisar ta dinkin duniya a Somalia a da, amma bayan watanni hudu, gwamnatin kasar ta kore shi, a lokacin da ya yi yunkuri shiga tsakanin a matsayin wakilin tsohon shugaban kungiyar Al Shabab, wanda ya so ya tsaya takara a zaben kasar ta Somalia, amma hukumar zaben kasar ta hana shi.

A dai ranar Litinin din da ta gabata, kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, ya yi Allah wadai da juyin mulkin na Sudan, ya kuma ba dakarun kasar wa’adin kwanaki goma sha biyar, da su mika mulki ga gwamnatin wucin gadi karkashin jagorancin farar hula.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG