Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Yi Kira Ga Bangarorin Syria Da Su Guji Tsunduma Yaki


Turkey Syria Idlib

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga bangarorin Syria su guji tsunduma yaki gadan gadan.

Guterres ya shaidawa manema labarai jiya Talata cewa, “Idlib ne gari daya tilo da ya rage daga cikin yankunan da aka haramta tada hankali a Syria, kuma bai kamata a maida wurin wurin da ake zubar da jini ba.”

Kimanin farin kaya miliyan uku ne ke zaune a arewa maso yammacin yankin, kuma MDD ta sha gargadin cewa za a jefa al’umma cikin matsanancin kuncin rayuwa idan aka kai harin soji a wurin.

Rasha da Iran da kuma Turkiya sune aka dauka a matsayin kasashen dake tabbatar da kiyaye yarjejeniyar haramta bude wuta a yankin. Sune suka sa ido wajen kulla yarjejeniyar kebe yankunan a Syria da zai zama mafi kwanciyar hankali ga farin kaya. Yankunan sun hada da Idlib, da Hama da gabashin Gouta da kuma kudancin Syria. A halin yanzu dai, Idlib kadai ta rage inda ake kiyaye wannan yarjejeniyar, sojojin sun kwace sauran garuruwan, suka maidasu karkashin ikon gwamnati.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG