Bayanan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa yawan al'ummar kasar Amurka ya haura miliyan 322 yayinda Najeriya ke da mutane miliyan 180.
Sauran kasashen da Majalisar Dinkin Duniya tace al'ummominsu na karuwa sun hada da Dimukradiyar Kwango, Pakistan, Habasha, Tanzania, Amurka, Uganda da Indonesia.
Majalisar tace za'a samu nikawar yawan mutane a kasashe 26 a nahiyar Afirka.
Akan kowane tasiri hakan ka yiwa kasashe irin su Najeriya, Malam Kasumu Garba Kurfi, masanin tattalin arziki dake kasuwar hadahadar saka hannun jari yace mai yawan al'umma yana da kasuwa saboda dole a ci dole kuma a rayu. A zamantakewar kasashe dole a dama da kasa mai yawan jama'a. Babu kasar da zata ce bata yi da India ko China.
Saidai ana bukatar yawan jama'a masu ilimi. Kamar China kowa aiki yake yi. Kowa na yin kokarin kirkiro wani abu.
A Afirka kamar Najeriya haihuwa kawai ake yi ba'a koyaswa sai daga baya su zama wa kasar bala'i su dinga haddasa tashe tashen hankali. Yace da babu tashin hankali amma yanzu mutane da yawa na cikin matsi. Wadanda basu da gida idan matasala ta taso sun kona gidan wani basu damu ba domin su basu da gida.
Samun yawan al'umma nada kyau amma dole mahukumta su maida hankali su tabbatar kowa ya samu ilimantarwa, horo, koyaswa da abun yi.
Taken bikin na wannan shekara shi ne bada tazara a haihuwa tsakanin mata masu haihuwa domin samar da al'umma nagari da cigaban kasa.
Rahoton Babangida Jibrin nada karin bayani.
Facebook Forum