Accessibility links

Me Ke Jawo Rigingimu Da Tashe-tashen Hankula?


Mutane sun taru a inda aka samu fashewar Bom a Kano. Talata Yuli. 30, 2013.

Malam Hussaini Attah daga birnin New York yayi bayanin abubuwan da ke jawo matsaloli a Najeriya.

Da yake tattaunawa da JummMalam Hussaini yace "Akwai mutanen da suka dauki addini sun mayar da shi son zuciya, basu da ilimi sai su ringa hukunci ta yin amfani da son zuciyarsu, suna gani kamar sun fi kowa."

Ya kara da cewa "Jahilci ne ya kawo wannan kashe-kashe da wasu ababen."

"Magance wannan matsala sai da addua, da kuma da yanda za’a yi a hada kan malamai a arewa, da matasa da shuwagabanni." in ji Malam Hussaini.

Da yake bada shawarwari, Malam Hussaini Attah cewa yayi "Malamai su ringa yin wa’azi na gaskiya."

"A ringa nuna wa yara addini da makomar tashin hankali da zub da jini a addinance."

Sannan ya rufe da cewa "A kafa tsari domin nuna wa matasa addini domin sun fahimci illar kashe-kashe da zub da jini."

XS
SM
MD
LG