Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ya Sa Aka Dage Ranar Dawo Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa-da-kasa a Najeriya?


Wani jirgin sama a kasar Ingila

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ranar da za a sake fara sufurin jiragen kasa-da-kasa bayan dage ranar da ta fara fitar wa domin dawo da zirga-zirgar.

A jiya Alhamis ne gwamnatin Najeriya ta dage sake maido da harkokin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa zuwa mako mai zuwa. A da gobe Asabar aka yi shirin bude tashoshin na kasa da kasa.

Darakta Janar na hukumar da ke kula da harkokin sufurin sama, NCAA, Musa Shu'aibu Nuhu ne ya bayyana hakan a jiya. A cewarsa ranar 5 ga watan Satumba mai zuwa ne ranar da suke sa ran fara zirga-zirgar sabanin 29 ga watan Agusta da suka fara zaba.

Ya alakanta dagewar da rashin kammala wasu ayyuka da basu shafe jiragen ba kamar yadda za a dinga yi wa mutane gwajin Covid-19 da kuma yanayin mayar da yin abubuwa ta yanar gizo.

An dakatar da harkokin jiragen saman ne watanni 5 da suka wuce a zaman wani bangare na kokarin yaki da annobar coronavirus.

A farkon makon nan Ministan harkokin jiragen sama na Najeriya Hadi Sirika ya fadi cewa za a sake maido da harkokin jiragen saman na kasa da kasa ne tunda ba a samu wasu da suka kamu da cutar COVID-19 a cikin jirage ba, biyo bayan bude harkokin jiragen sama na cikin gida da aka yi ranar 8 ga watan Yulin da ya gabata.

Sirika ya ce sake bude harkokin jirgin saman ya zo da matakai don tabbatar da cewa ba a samu koma baya ba a ci gaban da aka samu wajen shawo kan yaduwar cutar coronavirus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG