Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ya Sa Shugaban Karamar Hukumar Koko-Besse a Jihar Kebbi Ya Yi Murabus?


Kebbi na yaki da cin hanci da rashawa?

Shugaban karamar hukumar Koko-Besse Shu’aibu Ibrahim Koko ya yi murabus daga mukaminsa akan dalilan da ake gani suna da nasaba da yadda jihar sarrafa kudaden kananan hukumomin jihar

Rahotanni dake fitowa daga jihar Kebbi na sabawa juna akan musabbabin murabus din shugaban karamar hukumar Koko-Besse, Sha’aibu Ibrahim Koko.

Yayinda wasu ke cewa shugaban ya yi murabus ne saboda wawure kudaden kananan hukumomi da gwamnatin jihar keyi lamarin da ya sa yana ganin ba zai iya gudanar da harkokin karamar hukumar ba da kudi kalilan da ake basu.

Akwai wasu kuma da suka ce ya yi murabus ne saboda yunkurin tsige shi da kansilolinsa ke shirin yi.

Wani rahoton na cewa shugaban Sha’aibu Ibrahim Koko bai aminta ba ne da yadda ake basu umurnin karkata akalar kudaden kananan hukumomi zuwa wani asusun banki na kanin gwamnan jihar.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin shugaban mai murabus amma hakan bai yiwu ba. Sai dai wani na hannun damansa ya ce shugaban mai murabus ya sha alwashin ba zai yi magana da ‘yan jarida ba kan lamarin.

Akan haka Muryar Amurka ta tuntubi kwamishanan jihar mai kula da kananan hukumomi Garba Muhammad Dandiga dangane da batun kuma ya tabbatar cewa Shuaibu Ibrahim Koko lallai ya yi murabus don kansa. Ya ajiye mukamin ne ranar Talata da ta gabata watannin tara kacal da rantsar dashi a matsayin shugaban karamar hukumar Koko-Besse har na tsawon shekara biyu.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG