Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar da Kamfanin Sarrafa Shinkafa a Jihar Kebbi


Injin Sarrafa Shinkafa
Injin Sarrafa Shinkafa

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a yankin Afrika ta Yamma a Argungu ta jihar Kebbi.

Yace shirye shiryen gwamnatin tarayya a kan noma da habbaka tattalin ariziki sun fara samun nasara.

Shekaru biyu da suka gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da noman shinkafa a jihar Kebbi bisa sabo tsarin gwamnatinsa na fadada kafofin tattalin arzikin kasar da kuma rage dogaro akan albarkatun man fetur ta hanyar habbaka sha’anin noma.

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo yace yaje jihar ta Kebbi ne domin soma girbin amfanin shukar da shugaban kasar yayi idan aka yi la’akari da dimbin alfanon da kampanin zai kawo. Yace kafa wannan kampanin na jaddada muhimmancin sabon kudurin gwamnatin tarayya na baiwa masu zaman kansu damar taka muhimmiyar rawa a wajen kawo ci gaba ganin cewar kamfanin hannayen jari ne na mutane da dama wanda kuma zai samar da ayyukan yi da kuma kudaden shiga.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu yace koda yake yan Najeriya sun dan ji jiki sakamakon sabon tsarin gwamantin tarayya a kan noma da hana shigowa da abinci, kwalliya ta soma biyan kudin sabulu musamman a jihar ta Kebbi da wasu jihohin Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG