Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

YDG - Me Yasa Maza ke Kara Aure?


Tambayar da filin Yau da Gobe yayi kennan Juma'ar nan. Ga wasu daga cikin ra'ayoyinku.

“Dalilin dake sa malam bahaushe ke kara aure suna da yawa. Amma ya kamata ayi la’akari da cewa karin aure al’ada ce ta malam bahaushe. Domin duk duniyan nan babu inda maza (talaka, mai kudi da basarake) suke kara aure barkatai irin a kasar mu, koma in ce a Afrika. Sauran kasashen duniya har da kasashen larabawa kamar su Saudia ba’a samun karin aure kamar kasar Hausa. A wadannan kasashe sarakai da hamshakan attajirai ne ke karin aure kamar kasar Hausa. A wadannan kasashe sarakai da hamshakan attajirai ne kara aure ba talaka ba. Shi ma baya fin karin daya ko biyu. Amma anan namiji daya na kara mata har ya kai hudu. Allah ya kyuta.” – Kande Abashe

“Saboda Allah yayi umarnin yin karin auren ga namiji idan har yana iya yin adalci a tsakanin matan, ba lalle ne ace sai da rashin kyautatawa ne namiji yake iya kara aure ba, amma yana cikin dalilai wani lokacin, amma kuma yana iya kara aure koda ana zaune lafiya tsakanin maaurata idan yaga wata yana bukatar auren ta; addini ya hallatta masa. Ya kamata mata su fahimci cewa karin aure ibada ne, ba laifi bane. A rage zafin kishi, ba kyau.” – Zainab Ibraheem

“Wato akwai dalilai kamar haka:
*Rashin hakuri yana daga ciki.
*Matsalar Uwar Miji da Dangin Miji.
*Rashin auro Mata ta Gari ko Gidan Mutunci.” – Yusuf Yahaya

TAURARUWA

Anyi hira da Hafsat A. Ladan, marubuciyar littafin “Muguwar Sakayya,” game da tarihin ta da kuma kalubalen da take fuskanta a matsayin ta na Marubuciya a kasar Hausa.

GODIYA TA MUSAMMAN

Muna godiya ga mutanen da suka turo da ra’ayoyin su ta Facebook da Whatsapp. Muna kuma godiya ga duk wanda ya kira mu ta waya. Sai kuma ranar Litinin idan Allah ya kai mu inda zamu tattauna game da harkokin zamantakewar matasa.

TAMBAYAR LITININ (9/2/15)

Me za’a iya yi a gyara tarbiyyar matasa da tsaftace neman aure?

A kasance tare da shirin Yau da Gobe ranakun Litinin zuwa Juma’a bayan shirin Labarai na Rana.

XS
SM
MD
LG