Accessibility links

​Hantsi da karar harbe-harbe a Abuja ya saka jama’a da dama sauya hanya da ababen hawan su.

Da farko mutane sun kasance a rude, da ya kaiga yada jita-jita, gabannin fitar da sanarwa daga jami’ar hukumar leken asiri, wato SSS, Marilyn Orga dake nuna yunkuri ne arcewa daga gidan hukumar, da wadanda ke tsare sukayi.

Binciken da Dandali yayi, ya nuna cewa wadanda ke tsaren, sunyi wuf ne suka kwace bindigar wani mai raba abinci, shine har hakan ya jawo harbe-harbe a sanadin neman arcewa.

Zuwa yanzu babu cikakkiyar labarin rasa rayuka, ko ma nasarar arcewa na tsaren.
XS
SM
MD
LG