Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Menene Makomar Kauradda Ofishin Jakadancin Amurka Zuwa Birnin Kudus?


Ginin karamin ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus wadda Washington zata yi amfani dashi a matsayin ofishin jakadancinta na wucin gadi.

Ranar litinin Amurka zata kauradda ofishin jakadancinta zuwa birnin Kudus daga Tel-Aviv. Akalla mutane 800 ne zasu halarci bikin.

Da bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus ranar Litinin ga mai rai, yankin baki daya yana ajiyar zu ci na murna a gefe daya, da kuma zanga-zanga a daya bangaren.

Amurka tana shirin zata karbi bakuncin mutane kimanin 800 abikin bude ofishin jakadancin Amurkan a Isra'ila ranar Litinin. 'Yar shugaba Trump Ivanka, da mijinta Jared Kushner, zasu halarci bikin, yayinda shugaban Amurkan zai gabatar da jawabi ta vidiyo, inda zai sake jaddada alkawarin da yayi cikin watan Disemban bara na kauradda ofishin jakadancin Amurkan daga Tel-Aviv zuwa birnin kudus, ko Jerusalem da turanci.

Amma khaled Elgindy na cibiyar bincike kan fannoni daban daban a fadin duniya dake nan Amurka yace, "babu wani dalili na tsaro da yasa Amurka ta dauki wannan mataki, yace abunda yake faruwa akassin haka ne,yace yana jin matakin zai janyo rashin zaman lafiya a yankin, kuma hakan zai sa da wahala a gudanar da shawarwarin neman wanzarda zaman lafiya tsakanin yankin Falasdinu da Isra'ila.

Ahalinda ake ciki kuma, ma'aikatar kiwon lafiya a zirin Gaza tace an kashe ba falasdine daya, wasu 49 kuma sun jikkata lokacinda sojojin Isra'ila suka bude wuta kan masu zanga zanga kusa da shingen kan iyakar Isra'ila da kuma birnin khan-Younis a Gaza.

Ana zanga zangar ce gabannin bude ofishin jakdancin Amurka a birnin kudus ranar Litinin, da kuma cikar shekaru 70 da kafa Isra'ila.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG