Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

YDG – Meyasa Ma’aurata Suke Zuwa Wajen Bokaye?


Meyasa wasu ma'aurata ke zuwa wajen bokaye da malaman tsubbu don neman lafiyar saduwar miji da mata, maimakon s je wajen gogaggun likitocin da suka kware a kan ilimin lafiyar saduwar miji da mata? Ga takaitaccen sharhin sabon shirin Yau da Gobe.

“Rashin kulla aure bisa tafarkin musulunci, bidi'o'i sun yi yawa. Da za'a yi aure yadda manzon sallallahualaihi wasallam ya koyar gaskiya irin wadan nan matsalolin d sun kau.” – inji Zainab Ibraheem a Facebook.

“Yawancin mutane basu da ilimi saduwan kanshi balle su san yanda zasu yi shi yadda yakamata shi yasa suke zuwa neman maganin sun dauka shi zai saka su gamsu batare da kula da illar su ba.” – Binta Ba’abakalli a shafin WhatsApp.

“To muna godiya da wanna damar to hakikani gaskiya likitoci basuda kirikine yasa mutane basuso suje wojensu sai kaga kaja wojen likita sogoma amma koliya batabiya kudi sabuliba sene yasa mutane suka dukufa wojen bokaye.” – Sadu Sumana daga Facebook.

MATASA

Ibrahim Abdulaziz ya tattauna da matasan jahar Taraba game da cututtukan zamani da hanyoyin kamuwa da su.

GIRKI

Halima Abdullahi da Hajiya Hawwa sun bayyana mana yadda ake dafa abincin gargajiya me suna Tubani.

LAFIYA

Dakta Yashua Alkali Hamza, likitar kananan yara da matasa , kuma kwararriya a fannin kula da lafiyar jama’a da ke Abuja, ta bada amsa game da tambayar da mukayi mata a makon baya akan yawan mace-macen matan arewa a kan guiwa.

Dr. Mairo Mandara, kwararriyar likitar mata, masaniyar ilimin lafiyar saduwar miji da mata, kuma mai wakiltar gidauniyar Bill da Melinda Gates a Najeria ta bada cikakken bayani game da dalilan da suke sawa matan aure da dama basa gamsuwa wajen saduwa da mazajen su. Ta kuma bada shawara ga ma’aurata su rika zuwa gurin likita wajen neman taimako da maganin matsalolin da suka shafi lafiyar saduwar miji da mata.

Dr. Mandara ta kuma samu ta amsa kadan daga cikin tambayoyin masu saurare da suka kira mu kai tsaye.

A kasance tare da shirin Yau da Gobe ranakun Litinin zuwa Juma’a bayan shirin Labarai na Rana.

XS
SM
MD
LG