Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Michael Flynn Ya Amince Cewa Ya Shara Karya


Michael Flynn

Tsohoon mai baiwa shugaban Donald Trump shawara akan harkokin tsaro da aka sauke wani lokaci can baya ya amince cewa ya shara wa hukumar binciken manyan laifuka ta FBI,karya game da dangantakar sa da Rassia

Tsohon mai baiwa shugaba Donald Trump shawara a harkokin tsaro Janar maicheal Flynn mai ritaya , ya amsa cewa yayi laifi na shirga wa hukumar binciken manyan laifuka na Amurka wato FBI karya game, da binciken da akeyi na cewa kasar RAsha nada hannu wajen yin kutse a zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016.

Yanzu dai ya zamo Flynn shine jamii na farko a cikin gwamnatin Trump da ya amsa laifi game a binciken da ake yi karkashin mai bincike na musammam wato Robert Mueller.

Yau ne ranar kin dillaci ga Flynn, sailin da ya iso babban kotu dake nan birnin Washington DC domin sauraren tuhumar da ake masa.

Tsohon mai baiwa shugaban na Amurka shawara ya amince cewa ba shakka ya shara wa hukumar FBI karya game da dangantakarsa da jakadar kasar Rasha lokacin da ake hada-hadar mika mulki ga shugaba Trump kafin a rantsad dashi.

Shi dai Flynn yana cikin sahun farko na ‘yan gani kashe nin Trump a lokacin yakin neman zabe, kuma mai sukan abokiyar karawarsa Hillaru Clinton na jamiyyar Democrat.

Wasu daga cikin kalamar sa a wancan lokacin shine bamu bukatar shugaban da bata da kan gado wadda take jin tafi karfin doka, haka kuma yana cikin mutanen dake cewa a tabbatar an kai Hillary gidan yari.

Amma sai gashi a jiya jumaa, reshe ya juye da mujiya, domin sailin da Flynn ya fito daga cikin kotu sai jamaa na masa eho suna ku kulle shi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG