Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Michelle Obama Ta Kammala Ziyara Da Ta Kai Afirka


Uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama, da 'ya'yanata suke mamakin bayan sun hangi Giwa.

Bayan kammala ziyarar mako daya da ta kai kasashen Afirka biyu, dake kudancin nahiyar, uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama tana kan hanyarta ta dawowa gida.

Bayan kammala ziyarar mako daya da ta kai kasashen Afirka biyu, dake kudancin nahiyar, uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama tana kan hanyarta ta dawowa gida.

Lahadin nan jirgin Madam Obama ta tashi daga Botswana,bayan ta kammala ziyararta da tattaki zuwa wani gandun daji a kudancin Afirka.

Uwargidan Michelle, wacce ‘yayanta mata biyu ,da mahaifiyarta da ‘yayan dan’ uwanta suka rufawa baya, sun kalli giwa a wani gandun namun daji da ake kira Madikwe.

A lokacin ziyarar, madam Obama ta gana da shugabannin kasashen Afirka ta kudu Jacob Zuma da Ian khama na Botswana,da kuma wadanda suka sami lambar yabo ta Nobel Nelson Mandela da Desmond Tutu.

Haka ma a lokacin ziyarar madam Obama ta karfafawa matasa da mata guiwa kan shugabanci, da kuma kara fadakardawa kan cutar sida ko kanjamau.

Ana san ran zata iso nan Washington gobe litinin idan Allah ya kaimu.

XS
SM
MD
LG