Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Michelle Obama Ta Yi Wani Jawabi Mai Motsa Jiki


Michelle Obama
Michelle Obama

Michelle Obama, matar shugaban Amurka Barack Obama, tace kalaman batanci kan jikin mata dake fitowa daga bakin daya daga cikin ‘yan takaran shugaban kasa a zaben wannan shekara, magangannu ne “na cin zarafi, masu ban tsoro kuma wanda ke da ciyo” a wurin matan.

Matar shugaban kasar dai bata fito fili ta ambaci sunan Donald Trump a cikin jawabi mai motsa jiki da ta gabatar jiya a wajen wani taron yi wa Hilary Clinton kyampe ba, amma kowa ya san tana magana ne gameda zargin da wasu mata guda hudu suka fito suna yi ne, inda suka cewa Donald Trump ya taba jikinsu ba tareda amincewarsu ba.

Michelle Obama tace irin wadanan magangannun ba abinda ya kamata a rinka yi wa daukan kamar wani abinda aka saba da shi ne ba, kuma bai kamata a bari ana yinsu don kawai ana cikin hada-hadar siyasar zabe ba.

Shima Donald Trump ya zare dantse sosai wajen kare kansa daga wadanan zarge-zargen da matan suka yi mishi, wanda aka wallafa a manyan jaridun Amurka irinsu New York Times, Palm Beach ta Florida, Washington Post da kuma mujallar People Magazine.

Dan takarar yace duk wadanan matan makaryata ne kawai dake yi mishi kazafi don, a cewarsa, duk abinda suke fada ba daya da ya taba faruwa.

XS
SM
MD
LG