Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin kasashen duniya na ta ci gaba da aika sakkonin ta’azziya bayan mutuwar sarkin da akace yafi kowane sarki dadewa yana sarauta a duniya, watau Sarki Bhumibol Adulyadej, sarkin kasar Thailand.

wanda ya rasu yana da shekaru 88 a duniya, wanda akuma akace galibin mutanen kasarshi su milyan 67 basu taba sanin wani sarki ba, bayansa a duk rayuwarsu.

Marigayin sarki Bhumibol dai ya hau gadon sarautar kasar tasu yana matashi dan shekaru 18 ne kacal a shekarar 1946 – ma’ana ya share zunzurutun shekaru 70 ke nan cur yana sarautar kasar ta Thailand!

XS
SM
MD
LG