Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mikel Zai Koma Taka Leda A Ingila


John Obi Mikel

Tsohon kaftin din kungiyar Super Eagles ta Najeriya John Mikel Obi zai koma taka leda Ingila, lamarin da ya kawo karshen cece-kucen da ake yi dangane da makomar dan wasan a fagen kwallon kafa.

Mikel mai shekaru 33, zai koma kungiyar Stoke City da ke fafata gasar Championship, inda zai kasance dan wasa na 4 da kungiyar ta cefano a wannan bazara.

Manajan kungiyar Michael O’Neill ya bayyana farin cikin samun dan wasan, bayan kammala tattaunawa da kuma cimma matsaya da shi, inda dan wasan ya nuna bukatarsa na dawowa fafata gasar Premier, wanda kuma ya ke fatan yiwuwar hakan a kungiyar ta Stoke City.

John Obi Mikel
John Obi Mikel

Mikel ya kwashe tsawo shekaru kusan 11 a kungiyar Chelsea, inda buga mata wasanni fiye da 370, ya kuma sami nasarar lashe gasannin Premier, FA Cup, Europa League da kuma gasar Zakarun Turai.

Ya bar Chelsea zuwa kungiyar Tianjin Teda ta kasar China inda ya yi zama na dan lokaci, kana ya sake komawa Ingila a kungiyar Middlesbrough, kafin ya koma Trab-zons-por ta kasar Turkiyya.

Kwantaragin Mikel ya kai karshe ne sakamakon takaddama da ta barke tsakaninsa da shugabannin kungiyar a farkon somawar annobar coronavirus.

John Obi Mikel
John Obi Mikel

A matakin kasa kuwa, Mikel ya bugawa kasarsa ta Najeria wasa har sau 91, inda ya sami lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2013, ya kuma lashe lambar tagulla a gasar wasanni Olympics ta Rio a shekarar 2016.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG