Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Jama'a Zasu Kara Fuskantar Zafi Yau Lahadi A Amurka


Wata katuwar bishiya ta fado kan motar wani mutum mai suna Mike Wolfe a wani gari mai suna Falls Church a Jihar Virginia, dab da birnin Washington DC, bayan mummunan hadarin ruwan sama da iska, asabar 30 Yuni 2012.

Amma masana yanayi sun ce zuwa gobe litinin za a samu sauki yayin da wata iska mai sanyi daga Canada ta doso yankin tsakiyar Amurka

Miliyoyin jama’a a nan Amurka, su na jan damarar kara fuskantar zafi mai tsanani a yau lahadi, yayin da wani yanayi na zafin da ba a taba ganin irinsa ba ya buwayi yankunan tsakiya da kuma gabashin Amurka, yayi sanadin mutuwar mutane akalla 30.

Jiya asabar a nan birnin Washington, zafin da aka yi ya zarce awu 40 a ma’aunin Celsius, yayin da har yanzu wasu garuruwa da kauyuka da unguwanni a bayangari ba su da wutar lantarki fiye da mako guda a bayan da wata iska mai karfi da ruwan sama suka yi barna mai yawan gaske. Kamfanonin wutar lantarki da har yanzu ke aikin gyara layukan wuta da suka lalace ba dare ba rana, sun roki jama’a da su yi tsimin wutar lantarkin a saboda tsananin zafin da ake yi ya sa amfani da wutar ya cira sama ainun har yana barazana ga layukan dake kawo wuta.

Hukumar kula da yanayi ta Amurka ta ce ana kyautata zaton nan da gobe litinin za a fara samun saukin wannan zafi a yayin da wata iska mai sanyi fiye da irin wadda aka saba gani a wannan lokaci, zata fara fin karfin zafi a jihohin dake tsakiyar kasar nan. Wannan iska mai sanyi zata fito ne daga kasar Canada dake arewa da Amurka.

Masana yanayi sun ce ana sa ran hadarin ruwan sama mai karfi zai biyo bayan wannan iska mai sanyi, kuma zai iya janyo karin matsaloli a jihohin da har yanzu suke kokawar farfadowa daga hadarin ruwan sama da iska mai karfi da suka yi barna mai yawa a makon jiya.

XS
SM
MD
LG