Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UNICEF ya bayyana damuwa a game da mawuyacin halin da mata da yara kanana ke ciki a wasu yankunan jamhuriyar Nijar bayan da Majalisar Dinkin Duniya a jiya Laraba ta sanar cewa miliyoyin mutane, galibinsu yara kanana su na wahala sosai sanadiyar wasu tarin matsaloli da suka addabi kasar.
Kimanin mutane miliyan 2 da dubu 900 daga cikin mutane miliyan 21 na yawan al’ummar Nijar ne ke cikin halin kuncin rayuwa a yanzu haka a ewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya.
Kaka Touda Goni Mamadou, na kungiyar AEC ya ce matsalolin tsaro, da annoba da ambaliyar ruwa na da ga cikin dalilan da suka jefa yaran a cikin wannan yanayin.
Ganin yadda abubuwa suka tsananta, asusun na UNICEF ya nuna damuwa game da makomar wadannan yara dake cikin hali na rashin tabbas..
Da ma gwamnatin Nijar a karshen taron majalisar ministoci na ranar 14 ga watan Fabarairu ta sanar cewa ‘yan kasar da yawa na cikin yanayin bukatar tallafin gaggawa sakamakon rashin samun wadatar amfanin gona a daminar da ta gabata, lamarin dake shafar kauyuka 4,409 daga cikin 1,1726 da ake da su a kasar.
Mutane kimanin 263,000 ne suka tsere daga matsugunansu a cikin kusan shekaru 6 sanadiyar hare haren ta’addanci a yankin tafkin Chadi, yayin da wasu ‘yan Mali da ‘yan Nijar su 78,000 suka sami mafaka a yankunan Tahoua da Tilabery.
Wakiliyar UNICEF a Nijar Dr. Felicite Tchibindat ta ce shi ya sa ake bukatar kudi dala miliyon 60 domin tallafawa al’umomin yankunan dake ba 'yan gudun hijirar mafaka.
Asusun na UNICEF ya kuma gargadi hukumomin Najeriya kan halin kuncin rayuwar da miliyoyin ‘yan kasar ke ciki wanda akasarinsu mata da yara kanana ne, sakamakon yawaitar aiyukan ta’addancin 'yan kungiyar Boko Haram.
A saurari rahoto daga birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 26, 2021
Gwamnatin Nijar Ta Mayar Da Martani Game Da Tarzomar Zabe
-
Fabrairu 25, 2021
An Kama Masu Zanga Zanga Sama Da 200 a Nijar
-
Fabrairu 25, 2021
Ghana Ta Sami Kason Farko Na Rigakafin Coronavirus
-
Fabrairu 23, 2021
NIJAR: Bazoum Mohamed Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
-
Fabrairu 23, 2021
Wai Ko Wa Ake Ganin Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa A Nijar?
-
Fabrairu 22, 2021
Ana Jimamin Mutuwar Jami'an Zabe Bakwai Da Suka Rasu a Nijar
Facebook Forum