Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Mutane a Gabashin Afirka Na Fama Da Yunwa


Kasashe biyar na gabashin nahiyar Afirka na fama da matsalar karancin abinci biyo bayan samun damuna marakyau ta uku jere, a cewar cibiyar abinci ta MDD da kungiyar manoma ta duniya.

Yankunan kasashen biyar da suka hada da Somalia da Ethiopia da Kenya da Tanzania da kuma Uganda, baki ‘daya sun sami karancin ruwan sama.

Matsalar fari da suka samu hade da wata tsutsa mai lalata kayayyakin amfanin gona, sun bar miliyoyin mutane a gabashin Afirka cikin karancin abinci.

Duk kuwa da yawan samun lalacewar kayan amfanin gona da aka samu, an sami asarar dabbobi wanda hakan ya haddasa karancin madara.

Cibiyar MDD ta ce ana kyautata tsammanin halin da gandun daji da dabbobin da ake kiwo ke ciki zai ci gaba da tabarbarewa har sai watan Oktoba, lokacin da damuna zata sake zuwa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG