Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Nairori Sun Salwanta Sakamakon Hadarin Tankan Mai A Lagos


‘’Babban abinda yafi damu na shine yadda sakamakon jarabawata ta sakandare ya kone sakamakon gobarar da wannan hadarin tankan ta haifar ‘’

Wani daga cikin wadanda hadarin gobarar tankan mai ya afkawa Kenan dake cikin karamar hukumar idimu a jihar Lagos ke bayyana halin da suke ciki,bayan gobarar da ya faru sakamakon faduwar tankar man fetur, a daren asabar din data gabata.

Ko da yake ba wanda ya rasa ransa amma an tafka hasarar miliyon nairori domin ko a kididdigar da aka bayar ya nuna gidaje 34 ne da shaguna 70 suka kone kurmus.

Dada ko wane ne al’ummar da wannan balain ya afka mawa suke ciki? Kwanaki 3 bayan aukuwar sa.

Ga dai wata baiwar ALLAH mai suna Juliet ke cewa ‘’Sun taimaka mana sun bamu dubu 50domin samun suturar da zamu suturta jikin mu kana kuma suka ce zasu duba irin banner da wannangobarar ta haddasa muna’’

Akitek Abdullahi Ahmed Kabir shine shugaban hukumar kula da muhalli da kuma alkinta birnin Lagos yace gwamnati na iya bakin kokarin ta domin magance sake aukuwar wannan nan gaba. ga abinda yake cewa.

‘’Wannan matsala ce ta rashin man fetur shi yake jawo wannan cunkoso a wurare daban-daban sunzo diban mai sunyi layi da yawa sun cike ana fita nan ana fita can dole ka samu irin wannan hargitsin amma a tsarin birnin Lagos na tsare-tsaren ta abu ne da bai wai angama shi ba Kenan, kullun ana dubawa kuma ana kara inganta shi, ina maka alkawarin cewa ina cikin masu duba wannan tsare-tsare da kuma bada shawarwarin yadda ake inganta shi, ina maka alkawarin cewa wannan abu ne da zamu koma mu zauna mu duba mu kuma mu sake inganta shi idan irin wannan matsalar tazo ta samu bata yi ill aba ga al’imma da jamaan gari, musali akwai gidajen mai inda aka aka sasu, akwai shiri ma a kasa na cewa zamu tashi wasu gidajen man daga inda suke wasu kuma za a sasu su samar da wadataccen hanyar shiga gidajen man nasu, duka wadannan tsare-tsaren suna nan a kasa, kuma ina tabbatar maka cewa abu ne da dama ana dubawa kuma ana bincike akan wannan abu ana gyara akai kuma ba wai an gama bane, ina tabbata maka cewa zamu yi wannan aiki akai zamu tattauna akai za a nemi maslaha akansa’’

Su wadannan da abin ya rutsa dasu gwamnati tayi alkawarin taimaka musu kawo yanzu wani taimako tayi musu?

‘’A to ana nan ana tantance wadanda wannan matsalar ta rutsa dasu da iyalan su da wannan muhallin da irin barnan da aka samu a wadannan wurare shine abinda ake yi a yanzu, kuma kamar yadda shi mai girma gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode ya fada za a bada taimako iri-iri ga wadannan mutanen da wannanal’amari ya rutsa dasu’’

Gwamna Akinwumi Ambode wanda ya ziyarci wannan wuri da wannan hatsari ya auku ya shirya ganawa da shugabannin direbobin tankan man fetur domin kawo karshen irin wannan balai anan gaba.

Koda yake kungiyar direbobin tankan man fetur na kasa ta musunta zargin da ake mata na cewa yayan ta ke ganganci al’amarin dake haifar da wannan balai, kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar na kasa Alhaji Dayyabu Garga yake cewa ta hirar da akayi dashi ta wayan tarho.

‘’Direban da zai fita ya dauki mota ace ya samu hadari, mu kanmu abin ya dame mu kwarai da gaske, domin ba taba samun hadari akai-akai haka ba yana faruw a jifa-jifa, amma ace wannan ya faru ya faru gobe muma gaskiya ya daga muna hankali, saboda haka muma muna muna jiran hukuma tayi bincike a gano menene dalilin yin hakan, to koda yake idan abu ya faru wata sai kaga yana ta faruwa ubangiji ya jarrabe ku don haka wannan muna gani kamar jarabta ce daga Ubangiji, akwai lokacin da mu kai ta yawan samun hadarin jiragen sama a Najeriya, amma kuma a lokaci guda kome ya lafa ba alamun sa saboda haka muma muna fata namu tankokin nan gaba sai labari’’.

Wannan hadarin da ya faru a birnin Lagos wannan dai ba shine na farko ba a jihar, kuma a wasu sassan Najeriya, kwanaki biyu kafin aukuwar wannan balain irin wannan ya faru a garin Onisha inda mutane kusan 100 suka rasu, kuma ko a ranar lahadin nan data wuce yayin da ake jimamin aukuwar wannan hadarin sai kuma gashi an samu aukuwar hadarin tankar a cikin jihar ta Lagos a yankin titin lekki-Epe har ila yau dai a jihar ta Lagos, koda yake rahottani sun bayyana cewa ba a samu jikkata ba ko rasuwa ba, to ko akwai wani shirin inshore ne ne da yayan kungiyar ke samu? Game da irin wannan matsalar?

Anan ma ga abinda Dayyabu Garga ke cewa

‘’ A tsakanin mu da masu motocin akwai wani tsarin Inshora idan dai hadarin babu ganganci, idan direban ya samu rauni ko kuma ya rasa ransa akwai abinda ake ba iyalan sa idan kuma rauni ne wajen jinya asibiti akwai kaida wanda ake biya amma sai anyi bincike an gano menene dalilin hatsarin sailin shima ainihin mai motar kungiya zata same shi ya taimakawa iyalan direban idan har ALLAH yasa ya rasa ransa. Idan kuma wajen jinya ne mai motar zai taimaka wajen jiyar’’

To da yake jihar Lagos ta nemi ku zauna domin a samo hanyar magance wannan matsalar to me ake ciki yanzu haka?

‘’Mu a kullun kofar mu bude take a tattauna idan akwai matsala a samu maganin abin, zamu je mu saurari wannan jawabi da wannan jawabi da wannan ganawar da za ayi’’.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil adama karkashin sanannen lauyan nan Chief Femi Falana suka yi kira ga hukumomin dasu hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen haddasa hasaran rayukan al’umma ta ganganci musammam ma dai al’amarin da suka ce hakan zai kawo karshen hadduran dake faruwa wanda suke dangantawa da ganganci ta bangaren direbobi ko kuma bangaremn masu gidajen man fetur.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG