Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Minista Ta Ajiye Aikinta Sakamakon Fashewar Beirut


Hoton yadda fashewar Beirut ta hallaka birnin

Ministar Shari’ar kasar Lebanon, Marie-Claude Najm ta yi murabus daga mukaminta a wani abu da ake ganin na da alaka da fashewar da ta auku a kasar.

Najm, ita ce minista ta uku da ta ajiye aikinta tun bayan gagarumar fashewar da ta girgiza Beirut, babban birnin kasar a makon da ya gabata.

Da yammacin Lahadi Ministan muhalli, Demanios Kattar ya ajiye aikinsa inda ya kwatanta gwamnatin kasar ta Lebanon a matsayin “mai cike da rauni.”

Daga baya ne kuma Ministar yada labarai Manal Abdel-Samad ita ma ta ajiye aikinta.

Rahotanni na nuni da cewa, akwai ministoci da dama da su ma suke duba yiwuwar ajiye ayyukan nasu.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Lebanon
Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Lebanon

Tun a cikin makon da ya gabata ne masu zanga-zanga suka fantsama kan titunan birnin domin kira ga shugaban kasar Michel Aoun da ya ajiye mukaminsa sakamakon fashewar.

A yau aka shirya majalisar zartarwar kasar ta Lebanon za ta yi wani zama.

A gefe guda kuma, akalla ‘yan majalisar dokoki takwas ne suka bayyana cewa za su ajiye aikinsu yayin da majalisar ke shirin zama a makon nan.

Wani rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar na nuni da cewa akwai alamu masu nuna cewa dukannin jami'an gwamnatin za su iya ajiye aikinsu

A ranar Lahadi kasashen duniya suka yi alkawarin samar da kusan dala miliyan 300 ga kasar domin tallafa mata wajen farfadowa daga wannan ibtila’i da ya same ta, wanda ya yi sanadin mutuwar dumbin mutane.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG