Accessibility links

Minista ta Dauki Matakin Killace kan ta Bayan Mutuwar Direban ta Sanadiyar Ebola


Wani cikin sojojin da suka isa Liberiya domin yakar cutar Ebola.

Kafofin yada labaran kasar Laberiya sun ce ministar sufurin kasar ta dauki matakin killace kan ta bayan rahoton cewa direban ta ya mutu sanadiyar cutar Ebola.

Kafofin yada labaran kasar Laberiya sun ce ministar sufurin kasar ta dauki matakin killace kan ta bayan rahoton cewa direban ta ya mutu sanadiyar cutar Ebola.

Rahotanni sun ce ministar mai suna Angela Cassel-Bush ba ta kamu da cutar ba, amma dai don radin kan ta, ta dauki matakin sanya kan ta zaman kulle.

Ma'aikatar sufurin kasar ta Laberiya ta ce minista Cassell Bush ba ta sake ganin direban na ta ba tun 3 ga watan oktoba, ranar da yayi aikin shi na karshe. Rahotannin suka ce kwanai 21 da za ta yi a killace sun kama daga wannan rana ta 3 ga watan oktoban.

Ita ma babbar likitar gwamnatin kasar Laberiya, Dr. Bernice Dahn, kwanan nan ta fito daga zaman kulle kwanaki 21 bayan da sakatariyar ta ta musutu sanadiyar cutar ta Ebola.

A kasar Laberiya an tabbatar da cewa mutane fiye da 4,000 ne suka kamu da cutar Ebola kuma wadanda suka mutu sanadiyar cutar sun wuce 2,300 wadanda su ne alkaluma mafiya yawan da aka samu a wata kasar dake yankin dake fama da barkewar annobar cutar.

Jumlatan cutar ta hallaka mutane kimanin 4,450, akasarin su a kasar Laberiya da Guinea da kuma Saliyo.

A jiya Talata hukumar Lafiya ta Duniya, WHO/OMS ta yi kashedin cewa nan da zuwa watan Disamba ana iya samun sabbin kamuwa dubu 5 zuwa dubu 10 a kowane mako.

XS
SM
MD
LG