Accessibility links

Minista Ya Nemi Dalilin Tuhumar Mahaka Ma'adinai


'Yan sanda kewaye da gawarwakin mahaka ma'adinai masu zanga-zanga da suka bindige a Afirka ta Kudu

Ministan shari'a na Afirka ta Kudu, Jeff Redebe, ya nemi dalilin da ya sa za a tuhumi abokan aikin mamatan, a bayan da kowa ya san cewa 'yan sanda ne suka harbe su

Ministan shari’a na kasar Afirka ta Kudu, ya nemi lauyoyi masu gabatar da kararraki na gwamnati da su bayyana masa dalilin da yasa ake tuhumar mahaka ma’adinai da laifin kashe ‘yan’uwansu ma’aikata 34, wadanda a bisa dukkan alamu ‘yan sanda ne suka bindige suka kashe su.

Yau jumma’a ministan shari’a Jeff Redebe ya nemi da a ba shi wannan hujja, yana mai fadin cewa wannan shawara da hukumar gabatar da kararraki ta kasa ta Afirka ta Kudu ta yanke, ta girgiza da tsoratarwa tare da rudar da jama’a.

A jiya alhamis masu gabatar da kara suka tuhumi ma’aikatan ma’adinai su 270 a gaban kotu da laifin kisan kai, su na masu amfani da wata dokar da ba a santa sosai ba da ake kira “dokar hada kai ko aniya guda” wadda a karkashinta ana iya tuhumar mutanen dake cikin wani taro a zaman masu hadin baki idan aka aikata wani laifi cikin wannan taron.

A karkashin wannan doka da aka kafa tun zamanin mulkin turawa ‘yan wariyar launin fata, ana iya dora laifin mutuwar ma’aikatan ma’adinan, duk da cewa ‘yan sanda ne suka harbe su a wannan lamari na ranar 16 ga watan Agusta.

Masu gabatar da kara sun ce ala tilas ‘yan sanda suka yi harbi kan ma’aikatan hakar ma’adinan a saboda sun kai farmaki kan ‘yan sanda da adduna da kulakai. ‘Yan sanda suka ce ma’aikatan sun yi harbi akalla sau guda kan ‘yan sanda.
XS
SM
MD
LG