Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Ya Warke Daga COVID-19


Ministan harkokin hajen Najeriya, Geoffrey Onyeama
Ministan harkokin hajen Najeriya, Geoffrey Onyeama

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya warke daga cutar Coronavirus wacce ya yi akalla wata daya yana fama da ita.

Ministan ya bayyana hakan ne cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

"Ina son in bayyana wa duniya cewa da ikon Allah, sabon gwajin da aka min na COVID-19 ya bayyana cewa na warke daga cutar," in ji ministan.

Ya kuma mika godiyan ga 'yan uwansa da likitoci da kuma dukkanin wadanda suka taimaka masa da kuma yi masa addu'a.

A ranar 19 ga watan Yuli ne ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ya kamu da cutar bayan da ya rinka jin kaikayi a makogoronsa.

Lamarin kamuwarsa ya tayar wa mutane da dama a kasar hankali, musamman ma a shafukan sada zumunta kasancewar ba a dade da rasa babban jigo a gwamnatin kasar, Abba Kyari ba wanda ya rasu sakamakon cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG