Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Kiwon Lafiya Ya Zanta Akan Bullar Cutar Ebola a Jihar Rivers


Babban Ministan Kiwon Lafiya na Najeriya Onyebuchi Chukwu.

Yayin da Najeriya ke samun yabo daga kasashen duniya akan hobbasan da tayi na ganin ta dakile yaduwar cutar ebola sai gashi a karon farko wani likita ya rasu amma ba a Legas ba inda cutar ta fara, a jihar Rivers sanadiyar cutar ta ebola.

Ministankiwon lafiya na tarayyar Najeriya yace sun samu rahoton dake cewa ana zargin wasu da kamuwa da cutar a jihar Rivers.

Mutanen suna cikin wadanda suka tarbi Mr Sawyer ma'aikacin ECOWAS wanda ya shigo da cutar a Najeriya daga kasarsa ta asali Liberia. Mutanen sun yi cudanya da Mr Sawyer. Sun daukeshi sun kaishi asibiti da ma wasu wurare kafin ya mutu a asibiti.

Mutumin da ya kai cutar Fatakwal ma'aikacin ECOWAS ne kuma yana cikin wadanda ma'aikatar kiwon lafiya ta sama ido kafin ya sulale zuwa Fatakwal ya samu wani likita amininsa ya kula dashi. Shi likitan ne ya rasu. Da farko an dauka likitan ya mutu ne sanadiyar hawan jini sai da matarsa ta soma amai da zawo da zafin jiki fiye da kima. Ita ce ta fada cewa maigidanta yayi hulda da abokinsa dake dauke da cutar.

Bayan an lura ma'aikacin ECOWAS din baya nan an shiga nemansa. Daga baya suka kai koke ga hukumar da ta daukeshi aiki kana ta bayar dashi yanzu suna kula dashi. Amma sun samu tabbacin cewa likitan da ya rasu a Fatakwal ya rasu ne sanadiyar cutar ebola ba hawan jini ba. Shi kuma ma'aikacin ECOWAS yana da alamun yayi cutar ya warke.

Matar likitan da ya rasu da danta an killacesu ana basu magani tare da cigaba da sauran bincike.

Babu yadda za'a tsare mutumin da bai nuna alamun kamuwa da cutar ba. Yin hakan tamkar tauye masa hakinsa ne. Shi mutumin dake aiki a ECOWAS babban mutum ne kuma ba mahaukaci ba ne. Yasan abun dake faruwa domin haka bashi da hujjar zuwa Fatakwal a lokacin da yayi. Mutum mai zurfin tunane yakamata ya tsaya gidansa.

Ga cikakken rahoton Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:37 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG