Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Tsaro a Isra'illa Ya Nemi Afuwa Bayan Da 'Yan Sanda Suka Kashe Wani


Ministan tsaron Isra’ila ya nemi afuwa dangane da kisan da ‘yan sandan Isra’ila suka yi wa wani bafalasdine wanda ba ya dauke da makami kuma yake fama da wata larura ta rashin lafiya.

Harbin Iyad Halak, mai shekaru 32, a cikin tsohon birnin na Kudus a ranar Asabar, ya janyo suka daga jama'a sannan ya sake farfado da korafe-korafen da ake yi cewa, jami’an tsaro na amfani da karfin da ya wuce kima.

Benny Gantz, wanda shi ma firayim minista ne "na karba-karba" karkashin yarjejeniyar raba madafan iko, ya yi wannan jawabi a taron majalisar zartarwa da ake yi mako-mako na Isra'ila.

Ya kuma zauna kusa da Firayim Minista Benjamin Netanyahu, wanda bai ambaci abin da ya faru ba yayin jawabinsa na bude taron.

"Muna masu matukar bakin ciki game da lamarin da ya kai ga harbe Iyad Halak har lahira kuma muna jajantawa danginsa," in ji Gantz. "Na tabbata za a binciki wannan batun cikin sauri kuma za a cimma matsaya."

'Yan uwan Halak sun ce ba shi da cikakkiyar lafiya ne kuma yana kan hanyarsa ta zuwa makarantar masu larura ta musamman, inda yake zuwa daukan karatu a kullum a lokaci da aka harbe shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG