Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministoci 3 Sun Kamu da COVID-19 a Gambia


An tabbatar da ministoci uku a kasar Gambia sun kamu da cutar COVID-19, a cewar gwamnatin kasar.

Fadar gwamnatin Gambia ta fada a wani sakon twitter a ranar Lahadi cewa, ministan kudi Mambureh Njie da ministan fetur da makamashi Fafa Sanyang da kuma minister noma Amie Fabureh sun kamu da cutar corona.

Shugaban Gambia, Adama Barrow, ya sanar a makon da ya gabata cewa yana shirin killace kansa, bayan da gwaji ya tabbatar da mataimakin shugaban kasa Asatru Touray ya kamu da cutar.

Tun a cikin watan Maris ne dai Gambia ta kulle iyakokinta na sama da na kasa.

Gambia mai yawan al'umma da basu wuce miliyan uku ba suna da mutum 498 da suka kamu da COVID-19 kana tuni wasu mutum tara suka mutu da cutar a cewa John Hopkins.

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG