Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan Ma’aikatar Gona Ya kaddamar Da Babban Taro Da Kungiyar Miyatti Allah


A dai dai lokacin da ake ta samun kace nace tsakanin wasu al’ummar Najeriya dangane da samar da wuraren kiwo ga Fulani domin kwara da rigingimu da ake yawan samu tsakanin Fulani da manoma ko wasu al’ummar kasa.

Ministan ma’aikatar gona ta Najeriya Dr Audu Agbeh, ya kaddamar da wani babban taro da daruruwan mambobi na miyatti Allah a Najeriya, karkashin jagorancin shugaban kungiyar Alhaji Muhammad Kiro, Hardon Zuru, wanda taron yayi nazari akan matakan da suka kamata a dauka domin Shugaba Muhammadu Buhari ya cika alkawurran daya dauka na cewa za’a fitarwa da makiyayan wuraren kiwo domin kawo karshen matsalolin da ake samu.

Shugaban fulanin ya bayyana cewa lallai taron yana da muhimmancin gaske wurin share hawayen makiyaya daga sassa daban daban na Najeriya.

Hardon zuru ya kara da cewa taronne kadai zai magance matsalolin da suka ki ci suka ki cinyewa domin kuwa a cewar sa, wannan taro sakone daga shugaban kasa, domin ana sa ran zai sami halartar babban taron da za’a gudanar a cikin watan tara.

Daga karshe ya bayyana cewa idan za’a fitarwa da makiyaya makiyayunsu akan nka’ida kamar yadda ya kamata, babu bahillacen da zai kara zuwa ko’ina da za’a yi rigima da shi.

Yanzu dai an amince cewa a watan gobe shugaban kasa Muhammadu Buhari da kansa zai kaddamar da wannan gagarumin buki na shata iyokoki daban daban a yankunan dake duk fadin Najeriya inda makiyaya zasu sami damar yin kiwon sub a tare da samun matsaloli ko tashe tashen hankula tsakanin su da manoma ba.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG