Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Misirirawa sun ci gaba da zanga zangar neman komawa mulkin farin kaya


Wani mai zanga zanga yana gudu daga inda aka watsa barkonon tsohuwa
Wani mai zanga zanga yana gudu daga inda aka watsa barkonon tsohuwa

Masu zanga zanga kasar Misira sun yi fito mu gama da ‘yan sanda a birnin alkahira kwana hudu jere

Masu zanga zanga kasar Misira sun yi fito mu gama da ‘yan sanda a birnin alkahira kwana hudu jere, yayinda asuke neman a gaggauta gudanar da zaben shugaban kasa majalisar mulkin soji kuma ta mika mulki ga gwamnatin farin kaya .

Daruruwan ‘yan sandan kwantar da tarzoma dake gadin ma’aikatar harkokin cikin gida sun yi amfani da barkonon tsohuwa da harsashen roba yau lahadi domin hana masu zanga zangar dake jifa da duwatsu isa ginin. Masu zanga zangar suna zargin ma’aikatar da gaza daukar matakan da zasu hana aukuwar turmutsutsu da arangamar da tayi sanadin mutuwar mutane 74 bayan wani wasan kwallon kafa a birnin Port Said makon jiya..

Jami’ai suka ce a kalla mutane 12 aka kashe yayinda wadansu dubu biyu da dari biyar suka ji raunuka tunda tashin hankalin ya barke ranar alhamis.

Wadansu Misirawa sun hakikanta cewa, ragowar magoya bayan gwamnatin shugaba Hosni Mubarak ne suka haddasa tashin hankalin da aka yi a Port Said, suna kuma ganinshi a matsayin wata makarkashiyar tada rudani da nufin sake neman ikon fada a ji.

XS
SM
MD
LG