Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Misrawa Su Na Zaben Shugaban Kasa Yau Laraba


Ba a sa ran dan takara guda zai lashe zaben a zagayen farko, saboda haka an shirya gudanar da zagaye na biyu a ranakun 16-17 na watan Yuni

A yau laraba Misrawa suke gudanar da zaben shugaban kasa mai cike da tarihi, wanda masu binciken ra'ayoyi suka ce babu wani fitaccen gwani a tsakanin 'yan takarar da ra'ayoyinsu sun sha bambam kwarai.

Ba a sa ran cewa akwai dan takara guda da zai lashe wannan zabe a zagayen farko na kuri'un da za a kada a yau da gobe alhamis, a saboda haka an saka ranar 16 da 17 ga watan Yuni domin gudanar da zaben fitar da gwani a tsakanin mutane biyun da zasu fi samun kuri'u.

Manyan 'yan takara guda 4 sun kunno kai a tsakanin mutane 13 masu neman kujerar shugabancin kasar Misra, a ranar jajiberen wannan muhimmin gwaji na shimfida mulkin dimokuradiyya bayan mulkin kama karya na tsawon shekaru.

Biyu daga cikin mutanen dake kan gaba sun yi aiki karkashin tsohon shugaba Hosni Mubarak, kuma sun yi alkawarin maido da kwanciyar hankali tare da kawar da addini daga cikin sha'anin mulki.

Da alamun tsohon ministan harkokin waje, kuma sakatare-janar na Kungiyar Kasashen larabawa, Amr Moussa, mai ra'ayin sassauci, shi ne ke kan gaba. Amma a cikin 'yan kwanakin nan, kuri'un neman ra'ayoyin jama'a sun nuna tasowar Ahmed Shafiq, tsohon kwamandan mayakan sama, kuma firayim ministan karshe da Mr. Mubarak ya nada, wanda kuma yake samun goyon bayan rundunar sojojin kasar mai tasiri.

Mutanen biyu su na yin takara da wasu mutanen biyu masu kishin Islama.

Mohammed Morsi, wanda ke wakiltar kungiyar al-Ikhwanul Muslimun (Muslim Brotherhood) mai karfi da tasiri a kasar, bai shiga takara da wuri ba, amma ya ci gajiyar irin tsarin siyasa mai karfi na kungiyar dake bi gida-gida daga karkara har birni tana kyamfe.

Tashin gwauron zabin da yayi a farin jini ya dakushe tauraron Abdel Moneim Aboul Fotouh, dan kishin Islama mai sassaucin ra'ayi. Kyamfe na Aboul Fotouh, wanda tsohon dan kungiyar al-Ikhwanul Muslimun ne, yana maida hankali ne a kan masu jefa kuri'a dabam-dabam, daga masu sassaucin ra'ayi zuwa ga Musulmi Salafiyawa zuwa ga Kiristoci na kasar.

XS
SM
MD
LG