Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mitt Romney Zai Canja Salon Yakin Neman Zabe


Shugaba Barack Obama (hagu) da Mitt Romney su na yakin neman zabe
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican a Amurka, Mitt Romney, zai kaddamar da wani sabon babi na kyamfe yau litinin da nufin karkato hankulan jama'a da suka fara maida hankali kan shugaba Barack Obama.

Mr. Romney zai yi gangami a birnin Pueblo dake Jihar Colorado, kafin ya zarce zuwa ga muhimmiyar jihar nan ta Ohio inda zai yi rangadin kwanaki uku cikin motar bas daga gobe talata. Daga nan zai wuce Jihar Virginia. Dukkan jihohin nan uku su na cikin jihohin da ake kira "Fagen Daga" a zaben bana, a saboda har yanzu ba a san maci tuwo cikinsu ba, kuma su na da kuri'un da zasu iya bayar da nasara ga dan takarar da ya lashe su a zaben ranar 6 ga watan Nuwamba.

'Yan jam'iyyar Republican da dama sun soki Mr. Romney da laifin mayarda hankalinsa ga tarurrukan neman gudumawar kudin yakin neman zabe, maimakon fita yana neman kuri'un jama'a. Kimarsa ta fadi kasa a idanun masu jefa kuri'a a saboda wasu kura-kurai da katobarar da yayi ta tabkawa cikin 'yan makonnin nan.

A makon jiya, an fito da wani faifan bidiyo da aka dauka cikin sirri, inda aka ga Mr. Romney yana fadawa taron attajirai da suka hallara domin ba shi gudumawar kudin yakin neman zabe, cewa kusan rabin masu jefa kuri'a na Amurka dake goyon bayan shugaba Obama, dan takarar jam'iyyar Democrat, mutane ne da suke ganin kamar an kware su, sun dogara a kan gwamnati domin ta yi musu komai, kuma a cewarsa, "shi bai damu da su ba."

A halin da ake ciki kuma, shugaba Obama da mai dakinsa Michelle su na birnin New York a yau litinin, inda zai yi jawabi wajen bude zama na 67 na Babban Zauren Shawarwarin Majalisar Dinkin Duniya.

Mr. Obama da Mr. Romney zasu yi muhawarar farko tsakaninsu a ranar 3 ga watan Oktoba.
XS
SM
MD
LG