Accessibility links

Miyatti Allah Tayi Allawadai da Harin Sojoji Akan Fulanin Keana


Rugan Fulani

A wani taron manema labarai da kungiyar Miyetti Allah ta kasa ta kira a Abuja ta yi allawaai da harin da aka kaiwa rugagen Fulani a garin Keana cikin jihar Nasarawa.

Tun da aka ce sojoji sun kai hari kan rugagen Fulani a Keana kungiyar Miyetti Allah reshen Nasarawa ta yi alkawarin bin digdigin maganar har ma idan ta kama su je kotun kasa da kasa.

Jiya kungiyar Miyetti Allah ta kasa ta fara daukan matakin farko inda ta bayyana a ofishin manema labarai ta yi allawadai da harin da ta ce sojoji sun kai kan rugagen Fulani a Keana cikin jihar Nasarawa.

Muhammed Useini sakataren kungiyar a jihar Nasarawa yace suna zaune suka ga sojoji cikin motoci goma da tankunan yaki biyu. Sun shiga rugan Ardo Sodangi misalin karfe tara na safe suka yiwa dattabansu kisan gilla.

A wata kasida sanye da sa hannun kakakin sojoji Chris Olu Kolade yace mahukuntar kasar zasu yi bincike domin tabbatar da sahihancin zargin. Olu Kolade ya kara da cewa babu banbancin addini ko kabila a rundunar sojojin kasar. Chris Olu Kolade yace a mulkin dimokradiya kowa nada 'yancin fadin albarkacin bakinsa.

Mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah na daya Husaini Yusuf Baso yace tuni har sun fara aikin sulhu tsakanin 'yan kungiyar da alummomin jihohin Taraba, Binuwai, Kaduna, Katsina da Nasarawa. Yace suna da shugabanni a jihohi talatin da shida na Najeriya. Yace duk wata rikita rikita dake faruwa su ne suke shiga su yi sulhu. Yace sun dauki matakin ganin cewa an yi gyara kamar a Taraba inda mukaddashin gwamna ya nemesu. Sun je sun zauna da Fulanisu dake Ibi da kuma sarkin Ibi. Sun hadu da shugabanni a Takum da shugabannin kananan hukumomin Wukari da Takum. Sun fahimci matsalar Tiv da Fulani kuma sun bada shawara a yi anfani da shawarwarin da kwamitin Sarkin Musulmi ya bayar. A sa wuraren kiwo. Idan Bafillace ya shiga gona a kama shi ya biya amma ba wai a je a dauki ransa ba.

Kungiyar ta Miyetti Allah tana da ra'ayin kai kara a kotun kasa da kasa game da abun da ya faru a Keana.

Ga rahoton Medina Dauda.
XS
SM
MD
LG