Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Miyetti Allah Ta Yi Kira Ga Fulani


Miyetti Allah

A yayi da babban zaben Najeriya ke karatowa, kungiyoyin jama’a daban-daban suna ta kira ga mabiyansu game da gujewa fadawa rudanin siyasa.

Kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya reshen Minna a jihar Neja sun yi kira taron manema labarai don bayyana nasu kiran ga membobinta don gujewa tashin hankali da tada razoma.

Sun kuma nuna muhimmancin yin zaben cikin kwanciyar hankali. Alhaji Samaila Rebe shine shugaban kungiyar reshen jihar Neja ya kuma yi kira ga mutane musamman ma matasa game da bangar siyasa.

Ya yi kiran musamman ga matasan Fulani tare da neman su gujewa shaye-shaye da bangar siyasa don kar a kaisu a baro.

Game da goyon bayan fulnai da aka ce Fulani na yi da yawun kungiyar Kautel Hore sai Rebe ya nuna cewa kungiyarsu ta Miyetti Allah daban da Kautel Hore, don haka ya fadi cewa an musu katsalandan.

Inda yace Miyetti kungiyar makiyaya ce ba kungiyar siyasa ba. Ya bayyana cewa kowa yana da ikon zabar abinda yake so a siyasance amma a daina aron bakinsu ana ci musu albasa.

Daga karshe kuma sai shugaban ya sake tabo yadda barayin shanu ke damun Fulani har ma ya bada misalin satar da aka yiwa ‘yan uwansu a kwanan nan. Ya jadda cewa Myetti Allah bata taba kutsa kai a siyasa ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG